Najeriya-Faransa

Gwamnatin Najeriya ta nuna alhinin ta biyo bayan kisan jami'an kungiyar ACF

Wasu daga cikin makaman da yan kungiyar Boko Haram ke amfani da su a dajin Sambisa
Wasu daga cikin makaman da yan kungiyar Boko Haram ke amfani da su a dajin Sambisa via SK Usman facebook

Majalisar Dinkin Duniya da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari sun yi Allah wadai da kisan gillar da aka yiwa ma’aikatan agajin kungiyar ‘Action Against Hunger’ guda 4 ranar juma’ar da ta gabata a Najeriya.

Talla

An dai kama wadannan ma’aikatan ne a watan Yuli lokacin da suke kan hanyar su ta zuwa Damasak domin kai kayan agaji ga mabukata.

Umar Abba Gana, dan uwa ne ga Mohammed Abba Gana, daya daga cikin wadanda aka kashe, kuma ga abinda ya shaida mana.

Dan uwan daya daga cikin ma'aikatan kungiyar ACF da yan boko haram suka kashe

                                              A daya wajen wamni malamin kwalejin ilimin Gashua dake Najeriya Bitrus Bwala tare da wasu mutane 10 da kungiyar boko haram tayi garkuwa da su, sun bukaci gwamnatin Najeriya da ta yiwa Allah, ta kubutar da su daga hannun kungiyar.

Wani faifan bidiyo mai tsayin minti guda da rabi da kungiyar boko haram ta yada, ya nuna malamin da wadanda akayi garkuwa da su suna cewa su akasarin su kristoci ne daga Jihar Yobe, kuma suna bukatar kungiyar kristocin Najeriya ta taimaka wajen kubutar da su.

Bwala yace an kama shi ne ranar 27 ga watan Nuwamban wannan shekara, lokacin da yake hanyar zuwa wurin aikin sa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI