Tattaunawa da Ra'ayin masu saurare

Ra'ayoyi kan tasirin dakarun kasashen ketare wajen yakar ta'addanci a Sahel

Sauti 14:47
Daya daga cikin dakarun Faransa dake yakar ta'addanci a Tin Hama, a kasar Mali.
Daya daga cikin dakarun Faransa dake yakar ta'addanci a Tin Hama, a kasar Mali. REUTERS/Benoit Tessier/File Photo

Taron shugabannin kasashe 5 na yankin Sahel da ya gudana ranar lahadi a birnin Yamai na Jamhuriyar Nijar, ya jaddada muhimmancin ci gaba da hulda da kasashen duniya don yaki da ta’addancin a yankin na Sahel.Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da, a wasu kasashe aka fara nuna shakku dangane da irin rawar da dakarun kasashen yammacin duniya ke takawa a wannan yaki.Menene ra’ayoyinku game da amfani ko rashin amfani dakarun kasashen ketare a wannan yaki?Anya yankin Sahel zai iya tabbatar da tsaron kansa ba tare da gudunmuwar kasashen ketare ba?Kan wannan batu muka baku damar tattaunawa da musayar ra’ayoyi.