Wasanni

Barca ko Real Madrid?

A Classico Barcalona za ta ketse reni da Real Madrid a filin wasa na Camp Nou inda aka dau matakan tsaro da suka dace domin kaucewa duk wani tashin hankali ,a dai-dai lokacin da wasu kungiyoyi ke ikirarin kawo cikas a wannan wasa.

Lionnel Messi na Barcelona  da Karim Benzemadaga Real Madrid
Lionnel Messi na Barcelona da Karim Benzemadaga Real Madrid rfi
Talla

Mai horar da kungiyar Real Madrid Zinedine Zidane ya na mai cewa tabas, wannan wasa za ta sake basu damar duba ci gaba da aka samu a Real Madrid, yan wasan sa za su yi kokarin tsawon wasar don ganin sun kai kungiyar Real Madrid ga samun nasara.

Zidane ya tabbatar da cewa ya na da yekini yan wasan Real Madrid za su yi nasara.

Mai horar da kungiyar ta Barca Ernesto Valverde a lokacin da yake ganawa da manema labarai ya bayyana cewa yan wasan Barcelona na a shirye, tarihi ya nuna cewa Barca ba kanwar lasa ba ce.

Akala yan kalo sama da milyan 650 ne wani bincike ya gano cewa za su kali wannan wasa daga sassa daban daban na Duniyar na a dai dai lokacin da kungiyoyin Barcelona da Real Madrid kowanen su keda maki 35.

Za a dai baza akalla jami’an tsaro dubu 3 a harabar filin wasa na Camp Nou dake da kujeru kusan dubu 100, jami’an da za su mayar da hankali domin bayar da tsaro da kuma kare lafiyar yan kalo.

Shugaban kungiyar ta Barcalona Jose Maria Bartomeu ya ce babu ta yada za a fuskanci wata barazana sabili da haka mutane su daina kawo rudani dangane da wasar ta Classico.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI