Afrika

Majalisar wakilan taki amincewa da bukatar sauya kundin tsarin mulki

Shugaban Najeriya Mahamadu Buhari, na karbar takardar takara da wata kungiyar matasa ta saya masa 11-09-2018
Shugaban Najeriya Mahamadu Buhari, na karbar takardar takara da wata kungiyar matasa ta saya masa 11-09-2018 channeltv

Majalisar wakilan Najeriya taki amincewa da bukatar sauya kundin tsarin mulki domin sanya wa’adi daya na shekaru 6 ga shugaban kasa da gwamnonin kasar.Kudirin dokar wanda Dan Majalisa John Dyegh daga Jihar Benue ya gabatar, ya kuma samu goyan bayan Olajide Abdulraheem, ya tsallake karatun farko, kafin Majalisar tayi watsi da shi bayan karatu na biyu.

Talla

Masu sharhi a siyasar Najeriya na kallon cewar, takaita wa’adin zuwa guda na shekaru 6 na iya baiwa zababbun shugabanni damar mayar da hankali kan ayyukan dake gaban su ba tare da tunanin sake tsayawa takara ba.

Akasarin yan siyasa a Najeriya basu amince da haka ,wanda zai iya janyo koma baya ga lamuran da suka jibanci siyasa .

Kudin tsarin mulkin kasar na baiwa Shugaban kasa wa'adi na shekaru hudu sau biyu yanzu haka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.