Nijar ta yi bikin cika shekaru 61 da zama Jamhuriya
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Yau 18 ga watan Disemba Jamhuriyar Nijar ke bikin cika shekaru 61 da zama Jamhuriya, dama ce ga shugaban kasa na gabatar da jawabi ga al’ummar kasar kan halin da ake ciki.
A jawabi da Shugaban kasar Mahamadou Issoufou ya gabatar zuwa yan kasar ,ya na mai bayyana sabin matakan da gwamnatin kasar tadau domin tabbatar da tsaro da kuma sake karfafa hulda da wasu kasashe dangane da yaki da yan ta'adda masu ikirarin jihadi a yankin Sahel.
Shugaba Issoufou ya bayyana tsarin samar da cimaka mai rahusa , tsarin da gwamnatin Nijar za ta mayar da hankali ganin karancin abinci ko cimaka da ake fuskanta a wasu sassan kasar.
A karshe Shugaban kasar ya jaddada aniyar sa ta sauka daga karagar mulki tareda shirya zabe cikin lokaci da kuma mika mulki zuwa zabbaben Shugaban kasa .
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu