Najeriya

Buhari ya ba maidakin Ngige mukamin babbar sakatariya

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya rantsar da manya sakatarori 9 na ma’aikatun gwamnatin tarayya a fadar gwamnati dake Abuja.

shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.
shugaban Najeriya Muhammadu Buhari. AFP/Bertrand Guay
Talla

An rantsar da manyan sakatarorin ne gabanin taron majlisar zartaswar kasar na tsakiyar mako.

Cikin wadannan sakatarorin akwai maidakin ministan kwadago da samar da aikin yi na kasar Dokta Chris Ngige, wato Dokta Evelyn Ngige wacce ke wakiltar yankin kudu maso kudancin kasar.

Sauran manyan sakatarorin kuwa sune: Musa Hassan daga jihar Borno, Ahmed Aliyu daga Neja, Olushola Idowu (Ogun), Andrew Adejoh (yankin arewa ta tsakiya) da Umar Tijjani, daga yankin arewa maso gabashin kasar.

Sauran sun hada da Nasir Gwarzo (arewa maso yammacin kasar); Nebeolisa Victor Anakali (kudu maso gabas); Fashedemi Temitope Peter (kudu maso yamma.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya ya ruwaito cewa ana gama rantsar da manya sakatarorin ne, shugaban Najeriyan da ‘yan majalisarsa da sauran ministoci suka fara taron majalisar kasar na karshe a cikin wannan shekarar da muke ciki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI