Wasanni-Kwallon kafa

NFF za ta dakatar da Kano Pillars

Wasu daga cikin 'yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars.
Wasu daga cikin 'yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars. Naija news

Hukumar kwallon kafar Najeriya ta NFF ta yi barazanar dakatar da kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars tare da haramta mata shiga duk wata gasa a fadin kasar.

Talla

Har wa yau hukumar ta NFF ta ce za ta dakatar da hukumar Kwallon kafar jihar Kano, daga shiga dukkanin sha'anin kwallon kafa a fadin jihar.

Wannan dai ya biyo bayan wata kara da wani mai suna Salisu Rabiu ya shigar da hukumar a gaban babbar kotun jihar Kano ne, inda ya ke kalubalantar zaben shugabannin hukumar reshen jihar Kano, abin da yasa kotun ta bada umurnin cewa zababbun shugabannin su dai na bayyana Kansu a matsayin shugabannin hukumar kwallon a Jihar Kano.

Wata sanarwa da Sakataren NFF na Najeriya Dokta Muhammad Sunusi ya sanya wa hannu ta ce, haramun ne wani ya kai duk wata kara da ta shafeta zuwa kotunan gama gari, sabanin hukumar FIFA ko CAF, ko kuma kotu ta musamman da ke kula da sabgogin da suka shafi wasanni.

Kuma aikata Hakan na cikin manyan laifuka da hukumar bata wasa dasu.

Hukumar ta NFF ta bawa masu karar wa'adin kwanaki bakwai da su janye karar ko kuma ta zartar da hukuncin da ta tanadar cikin dokokin na ta.

Yanzu haka dai wasan da Kano pillars za ta buga da Ifeanyi Ubah a ranar Lahadi na cikin kila wakala.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.