Faransa-Mali

Dakarun Faransa sun kashe 'yan ta'adda 33 - Macron

Shugaban Faransa Emmanuel Macron
Shugaban Faransa Emmanuel Macron REUTERS/Charles Platiau

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya ce ‘yan ta’adda 33 ne suka mutu a wani hari da dakarun kasarsa suka kaddamar a tsakiyar kasar Mali a Asabar dinnan.

Talla

A wani jawabi da ya gabatar ga al’ummar Faransa mazauna Ivory Coast, shugaba Macron ya ce dakarun na Faransu, sun kubutar da wasu jandarmomi da ‘yan ta’addan suka yi garkuwa da su a birnin Mopti.

Macron wanda ke ziyarar Ivory Coast don yin bukuwan Kiristimati da sojojin kasar dake yaki da ‘yan ta’ada ya ce Faransa za ta bullo da sabbin dabarun yaki da masu tsatsaurar ra’ayin addini a yankin Sahel.

Tuni dai shugaba Macron ya gana tare da cin abincin dare da dakarun Faransa dubu guda da ke sansanin Sojin birnin Abidjan mallakin Faransar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI