Afrika

Amfani da kudin CFA ya kawo karshe a Afrika

Takardar kudin CFA
Takardar kudin CFA alamy.com

Bayan share kusan shekaru 74 suna amfani da takardar kudin CFA wacce Faransa ce ta samar da ita tun lokacin mulkin mallaka, a yanzu, kasashen 8 na yammacin Afrika da ke amfani da wannan kudi, za su kawo karshen dogoro da baitul malin Faransa a cikin shekara mai zuwa, tare da canza wa kudin na cfa suna zuwa ECO.

Talla

Shugaban Cote d’Ivoire Alassane Ouattara da ke matsayin jagoran Majalisar Gudanarwar Kasashen 8 da ke amfani da kudin cfa a yammacin Afirka ne ya sanar da haka, lokacin da yake ganawa da shugaba Emmanuel Macron na Faransa a birnin Abidjan.

Kuna iya latsa alamar sautin da ke kasa domin sauraren rahoton Salissou Hamissou kan wannan batu.

Amfani da kudin CFA ya kawo karshe a Afrika

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI