Ana neman tsohon madugun 'yan tawaye ruwa a jallo
Wallafawa ranar:
Mai shigar da kara na gwamnatin Cote d’Ivoire, Richard Adou ya fitar da sammacin kama tsohon madugun ‘yan tawaye kuma tsohon shugaban majalisar dokokin kasar, Guillaume Soro bisa zargin shirya wa kasa zagon-kasa da kuma handame dukiyar da ta kai CFA milyan dubu daya da milyan 500.
A ranar Litinin ne ya kamata Soro ya koma Abidjan bayan ya sanar da aniyarsa ta tsayawa takarar shugabancin kasar, amma saboda wannan sammaci aka karkata akalar jirginsu zuwa Accra na kasar Ghana.
Soro wanda ya shafe watanni 6 a ketare, ya zarce Accra ne a daidai lokacin da jami’an tsaron Cote d’Ivoire suka yi cincirindo a shalkwatan jam’iyyarsa da ke birnin Abidjan.
‘Yan sandan sun kama mutane 15 daga cikin magoya bayan Soro da suka hada da wani na hannun damansa, Alain Lobognon, inda aka tuhume su kan aikata mabanbantan laifuka.
Wannan dambarwa na zuwa ne a yayin da ake shirin gudanar da zaben shugabancin kasar a cikin watan Oktoban shekarar 2020, zaben da ake fargabar za a gudanar cikin dari-dari.
Akalla mutane dubu 3 suka rasa rayukansu sakamakon tarzomar bayan-zabe a shekarar 2010-2011 a Cote d’Ivoire.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu