Fafaroma Francis ya bukaci wanzar da zaman Lafiya a duniya

Fafaroma Francis a garin hiroshima
Fafaroma Francis a garin hiroshima Vincenzo PINTO / AFP

Shugaban Darikar Katolika ta Duniya, Fafaroma Francis ya bukaci al’ummar duniya da ta samar da hasken da zai kawar da duhun da ke kunshe a zukatan bil’adama wanda shi ke ummul aba’isin zalunci da rashin adalci har ma da rikice-rikice da kuma matsalar kin-jinin bakin haure a cewarsa. 

Talla

A yayin jawabinsa na ranar Kirismai a fadar Vatican, Fafaroman mai shekaru 83 ya bukaci wanzar da zaman lafiya a kasashen Syria da Lebanon da Yemen da Iraqi da Veneuela da Ukraine da kuma wasu sassa na Afrika da ke fama da tashe-tashen hankula.

Kuna iya latsa alamar sauti da ke kasa domin sauraron abin da Limaman addinin na kirista a Najeriya da Nijar ke cewa dangane da wannan buki, cikin shiri na musamman kan bukukuwan kirsimeti tare da Ahmed Abba.

Shiri na musamman kan bukin kirsimeti 2019

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI