Burkina Faso

Harin ta'addanci ya hallaka mata 35 da Sojin Burkina Faso 7

Dakarun Sojin Burkina Faso.
Dakarun Sojin Burkina Faso. AFP PHOTO/ISSOUF SANOGO

‘Yan ta’adda sun hallaka fararen hula 35 galibi mata yayin farmakin da suka kaddamar kan wani kauye da ke arewacin Burkina Faso, harin da ke matsayin mafi muni da al’ummar kasar suka gani tun bayan tsanantar hare-haren ta’addanci a kasashen saharar Afrika cikin shekarar 2015.

Talla

Harin na zuwa bayan makamancinsa da ‘yan ta’addan suka kai kan sansanin Sojin kasar na Arbinda da ya hallaka soji 7 duk dai a jiya Talata, ko da dai a martanin da Sojin na Burkina Faso suka mayar sun yi nasarar hallaka ‘yan ta’adda 80.

Rahotanni sun bayyana cewa an shafe kusan sa’o’i 7 ana musayar wutar tsakanin Sojin na Burkina Faso da ‘yan ta’addar masu ikirarin jihadi a sansanin na Arbinda da ke yankin Soum wanda daga karshe Sojin suka yi nasarar hallaka ‘yan ta’addan 80.

Yankunan kasar ta Burkina Faso da ke da iyaka da Mali da Nijar na ci gaba da fuskantar barazanar tsaro musamman kan Sojin kasar da kuma kananun kauyuka wanda kawo yanzu ya hallaka daruruwan mutane baya ga tilastawa wasu dubunnai barin gidajensu.

A wata sanarwar ma’aikatar tsaron Burkina Faso ta ce wani ayari na ‘yan ta’addan ne dauke da makamai suka farmaki sansanin Sojin da yammacin jiya Talata yayinda wani ayarin na musamman kuma ya farmaki fararen hula da ke kauyukan gab da sansanin.

Ka zalika sanarwar ta ruwaito Shugaba Roch Marc Christian Kabore na yabawa kokarin Sojin da kuma jajantawa wadanda harin ya yi sanadin rasa rayukansu.

A cewar sanarwar cikin fararen hulan 35 da ‘yan ta’addan suka kashe 31 mata ne sai mutum 4 maza baya ga wasu 6 da suka jikkata.

Sanarwar ma’aikatar tsaron ta Burkina Faso ta kuma bayyana adadin sojinta 20 da suka samu raunuka yayinda da ta ayyana sa’o’i 48 don makokin wadanda suka rasa rayukansu a ilahirin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.