Najeriya

Sarkin musulmi ya mayar da martani ga kungiyar Kiristocin Najeriya

Mai alfarma sarkin musulmi a Najeriya Sultan Muhammad Sa’ad Abubakar III ya mayar da martani ga ikirarin kungiyar kiristocin kasar CAN da ta kafa hujja da wani rahoton Amurka inda ta ce Kiristoci a kasar na fuskantar muzgunawa.

Mai alfarma sarkin musulmi Alhaji Muhammad Abubakar Sa'ad.
Mai alfarma sarkin musulmi Alhaji Muhammad Abubakar Sa'ad. Daily Trust/Nigeria
Talla

Kungiyar ta CAN ta goyi bayan rahoton na Amurka da ya sanya Najeriya a jerin kasashen da ke hana ‘yancin gudanar da addini.

Sai dai a martanin Mai alfarma sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar ya ce ya girgiza matuka da yadda CAN ta goyi bayan rahoton na Amurka har ma da karin kafa wasu hujjoji kan yadda ake cin mutuncin mabiya Kiristan.

A cewar mai alfarma sarkin musulmi ko kadan rahoton na Amurka ba abin karba ba ne, don kuwa baza a iya jeranta Najeriya a sahun kasashen da ke zuba ido ana cin mutuncin wani addini ba.

Tun a ranar 18 ga watan nan na Disamba ne, wani rahoton Amurka ta bakin sakataren harkokin wajenta ya sanyo Najeriyar a sahun kasashen da ke hana ‘yancin gudanar da addinai, rahoton da CAN ta yi maraba da shi da hannu bibbiyu.

Sauran kasashen da Amurka ta sanya a jerin wadanda ke hana ‘yancin gudanar da addinai akwai Burma kana China da Eritrea da Iran da Korea ta Arewa da Pakistan da kuma Saudi Arabia baya ga Tajikistan da kuma Turkmenistan.

Sauran a cewar rahoton na Amurka sun hadar da Comoros da Rasha baya ga Uzbekistan kana Cuba Nicaragua da Najeriya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI