Najeriya

Yadda aka yi cushe a kasafin kudin Najeriya na 2020

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a majalisar dokokin kasr
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a majalisar dokokin kasr premiumtimesng

Lokacin da shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya gabatar da kudirin dokar kasafin kudin shekarar 2020 a gaban zaman hadin gwiwa na majalisar dokokin kasar, naira tiriliyan 10.3 ne ke kunshe a cikin kudirin.

Talla

Sai dai yayin da ya sanya hannu a kudirin don ya zama doka, ya sanya hannu ne a kan kudirin da ya kunshi jimillar kudi da ya kai naira tiriliyan 10.6, wato an samu karin da ya kai na naira biliyan 264.

Shugaban kwamitin kasafin kudi na majalisar dattawar kasar Ibrahim Barau, wanda aka fara jin wannan bayani daga bakinsa, ya ce anyi wannan cushe ne don toshe gibin da aka samu wajen samar da ayyuka a kasar.

Bayanai da alkalumma da jaridar Premium Times da ake wallafawa a Najeriyar ta samu na nuni da cewa babban birnin tarayyar kasar Abuja ya fi samun kaso mai tsoka a cikin hukumomi da ma’aikatun kasar a kasafin kudin bana.

Tun da farko shugaba Buhari ya kasafta wa Abuja naira biliyan ₦28.4, amma da kudirin kasafin kudin ya zama doka, sai jimillar kudaden ya karu zuwa naira biliyan ₦62.41.

Duk da cewa birnin Abuja na fuskantar kalubale sakamakon lalacewar da hanyoyi suka yi, za a yi amfani da naira biliyan ₦37 wajen gyarar majalisar dokokin kasar.

A shekara mai kamawa, gyarar ginin majalisar dokokin kasar kawai zai lakume kudade fiye da wadda hanyoyin gwamnatin tarayya a fadin kasar za su lakume.

Idan aka yi dubi da gaba daya kasafin kudin, za a fahimci cewa kusan dukkannin ma’aikatu da ke kasar sun samu kari daga majalisar dokoki, abin da wasu masharhanta ke kira cushe.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.