Cote d'Ivoire

Guillaume Soro, zai shirya komawa gida Cote D'Ivoire daga waje

Guilluame Soro, Tsohon madugun yan Tawayen Cote D'Ivoire,kuma tsohon Shugaban majalisaar dokkokin kasar
Guilluame Soro, Tsohon madugun yan Tawayen Cote D'Ivoire,kuma tsohon Shugaban majalisaar dokkokin kasar Sia KAMBOU / AFP

Tsohon Madugun yan Tawayen Cote D’Ivoire ,kuma tsohon Shugaban Majalisar kasar Guillaume Soro da hukumomin kasar ke nema ruwa a jalo ,bayan bayyana takarar sa a zaben kasar na shekara mai kamawa, a wata zantawa da ya yi da jaridar kasar Faransa le Journal du Dimanche, Soro ya ce babu tanttama zai shirya gwagwarmaya don kawar da Shugaban kasar Alassane Dramane Ouattara daga Faransa.

Talla

Guillaume Soro ya bayyana cewa tabbas ,zai tsaya takara a zaben shugabancin Cote D’Ivoire, zai tsaya a matsayin jarumi tareda yin koyi da Janar De Gaulle mutumen da a wancan lokaci daga Landan ya kadammar da wani shirin na kwato Faransa daga hannun makiya.

Soro ya fuskanci fushin hukumomin Cote D'Ivoire da suka haramta masa shiga kasar a lokacin daya dawo daga balaguro ,lamarin da ya tislasawa jirgin dake dauke da shi sauka Ghana kafin daga bisali ya kama hanyar zuwa Turai.

Tuni dai ake ganin zai iya samun goyon bayan kungiyar Générations et peuples solidaires (GPS). Guillaume Soro ya bayyana aniyar tasa ta tsayawa takarar ne, a cikin wata hirar hadin guiwa da ta hadashi da kafafen yada labaran Faransa,

Kimanin shekaru 2 da suka gabata ne dai, aka samu baraka tsakanin Guillaume Soro da shugaba Alassane Ouattara, da ake ganin yana kokarin sake yin wani wa’adi na 3 a jere, duk da cewa bai furta haka ba, amma kuma bai kawar da yiyuwar sake tsayawa ba bayan da kundin tsarin mulkin kasar ya bashi damar yin haka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.