Kotun Sudan za ta rataye jami'an tsaron kasar 27 kan kisan farar hula
Wallafawa ranar:
Wata kotu a Sudan ta zartas da hukuncin kisa kan wasu jami’an sirrinta 27 da aka samu da hannu wajen kisa da kuma azabtar da masu zanga-zangar adawa da gwamnati cikin shekarar nan.
Kotun karkashin mai shari’a Sadok Albdelrahman ya ce jami’an an same su da hannu dumu-dumu wajen azabtarwa baya ga kisan wasu fararen hula ciki har da kisan Ahmed al-Kheir malamin makaranta, wanda jami’an hukumar suka kama cikin watan Janairun da ya gabata suka kuma hallaka shi a shalkwatarsu.
Kotun dai ta bukaci aiwatar da kisa kan mutanen 27 ta hanyar rataya bayan hujjoji da suka nuna yanda suka zabtar da tarin jama’ar kasar ta Sudan lokacin zanga-zangar wadda ta faro daga watan Disamban bara.
Akalla dai mutane 177 aka tabbatar da mutuwarsu a hannun jami’an tsaron kasar ta Sudan yayinda wasu aka harbesu da harsashi a dandalin zanga-zangar bayan da shugaban kasar na wancan lokaci Omar Hasan al-Bashir ya baiwa jami’an tsaro cikakken ikon ladabtar da masu zanga-zangar.
Wasu majiyoyi na daban dai sun bayyana cewa adadin mutanen da suka mutu a zanga-zangar sun haura mutum 250.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu