Farfesa Kabir Isa kan shirin Najeriya na janye sojinta a Maiduguri
Gwamnatin Nigeria ta sanar da aniyarta na tattara sojanta don barin yankin arewa maso gabashin kasar inda ake ta dauki ba dadi da ‘yan kungiyar Boko Haram a shekara mai kamawa don maida su inda ake matukar bukatar sojojin a kasa.
Wallafawa ranar:
Hafsan Sojojin ruwa na kasar Rear Admiral Ibok Ekwe-I0bas ya fadawa manema labarai haka jim kadan bayan xaman wakilan majalisar Tsaron kasar tare da shugaban Nigerian Muhammadu Buhari a Abuja.
Acewarsa Rundunar ‘yan sanda da jamian Hukumar tsaro na Civil Defense zasu ci gaba da sauran aikin kawar da mayakan na kungiyar Boko Haram.
Akan haka muka nemi ji daga Farfesa Mohammed Kabir Isa na Jamiar Ahmadu Bello da ke Zaria wanda yasha bincike da sharhi dangane da al’amarin Boko Haram a yankin arewa maso gabashin Najeriya, ko lokaci yayi na janye dakarun daga yankin.
Farfesa Kabir Isa kan shirin Najeriya na janye sojinta a Maiduguri
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu