Liberia

'Yan Adawar Liberia sun janye zangar-zangar kin jinin gwamnati

Masu zanga-zangar adawa da gwamnati a Liberia.
Masu zanga-zangar adawa da gwamnati a Liberia. CARIELLE DOE / AFP

Bangaren Adawa a Liberia sun janye daga zanga-zangar kin jinin gwamnatin da suka shirya gudanarwa yau Talata bayan wata ganawarsu da jami'an tsaro da suka ki amsa bukatarsu ta basu cikakkiyar kariya yayin gangamin.

Talla

Jagororin adawa a kasar ta Liberia dai sun ce za su gudanar da zanga-zangar ne domin kalubalantar halin da tattalin arzikin kasar ke ciki, sai mashirya gangamin sun ce akwai karancin tsaro da ake ganin zai iya shafar lafiyar daruruwan fararen hular da za su yi tattakin.

Bangaren adawar na Liberia na zargin shugaba George Weah da gazawa ta fannin tattalin arziki da samar da ayyukan yi, yayinda a bangare guda tsadar rayuwa ke ci gaba da ta’azzara a sassan kasar.

Rahotanni sun bayyana cewa Jami'an tsaron Liberia sun kafa sun tsare a yankunan jagororin masu zanga-zangar don hanasu fitowa yayinda a tsakiyar birnin Monrovia ma aka sanya matakan tsaro tun daga jiya Litinin.

Shugaban 'yan adawa na Liberia Yekeh Kolubah ya zargi George Weah da keta tanadin kundin tsarin mulkin kasar bayan da ya yi umarnin haramta kowacce irin zanga-zangar har zuwa bayan watan Janairu.

Sai dai bangaren adawar ya sanya ranar 7 ga watan Janairu don gudanar da zanga-zangar da nufin kalubalantar gwamnatin ta George Weah.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI