Guinea Bissau

Pereira zai kalubalanci sakamakon zaben Guinea

Domingos Simoes Pereira da ya sha kayi a zaben Guinea Bissau
Domingos Simoes Pereira da ya sha kayi a zaben Guinea Bissau Aylton Fernandes Crato Cá

Dan takarar jam’iyya mai mulki wanda ya sha kaye a zaben shugabancin Guinea Bissau a ranar Lahadi, Domingos Simoes Pereira, ya ce zai kalubalanci sakamakon zaben da ke tabbatar da Umaro Sissoco Embalo a matsayin wanda ya yi nasara.

Talla

Simoes Pereira ya ce, an tafka kazamin magudi a lokacin zaben da kuma wajen fitar da sakamakonsa, saboda haka zai shigar da kara don ganin cewa an soke wannan zabe.

Dan takarar adawa Umaro Sissoco Embalo ya samu sama da kashi 53% na kuri’un da aka kada a zaben.

Embalo ya bukaci daukacin al’umar kasar da su mara masa baya, yayin da ya ce, zai jagoranci shugabancin hadaka a kasar wadda ta yi fama da jerin juyin mulki tun bayan samun ‘yancinta daga Turawan mulkin Portugal a shekarar 1974.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.