Afrika

Shugaba Gnasingbe ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takara karo na hudu

Shugaban kasar Togo Faure Gnassingbé a birnin Lome na kasar Togo
Shugaban kasar Togo Faure Gnassingbé a birnin Lome na kasar Togo Yanick Folly / AFP

Yau laraba ce ranar karshe ga wadanda ke bukatar tsayawa takara a zaben shugabancin kasar Togo don su gabatar da takardunsu na takara ga hukumar zaben kasar dake babban birnin Lome.

Talla

Yan siyasa bangaren adawa na ci gaba da bayyana damuwa yan lokuta biyo bayan sanar da takarar Shugaban kasar Faure Gnasingbe,mutumen da ya gaji mahaifinsa wanda ya yiwa kasar rikon kama karya tareda murkushe duk wani bore daga bangaren yan adawa.

Zaben wanda za a yi ranar 22 ga watan fabarairu mai zuwa ne za a gudanar da zaben, kuma tuni shugaha mai ci Faure Gnasingbe ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takara karo na hudu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.