Madugun Tawayen Seleka ya koma gida

Tsohon shugaban Jamahuriyar Afirka ta Tsakiya Michel Djotodia, lokacin dawowarsa gida a birnin  Bangui, ranar 10 ga watan Janairu 2020
Tsohon shugaban Jamahuriyar Afirka ta Tsakiya Michel Djotodia, lokacin dawowarsa gida a birnin Bangui, ranar 10 ga watan Janairu 2020 FLORENT VERGNES / AFP

Madugun tawayen Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya kuma tsohon shugaban kasar Michel Djotodia ya koma birnin Bangui yau Jumma’a, shekaru 6 kenan bayan barin mulkin kasar, tare da neman mafaka a kasashen ketare.

Talla

Michel Djotodia mai shekaru 71, wanda ke jagorantar kungiyar tawayen Seleka, ya karbi mulkin jamhuriyar Afirka ta Tskiya da karfin tuwo a watan Maris din shekarar 2013.

Djotodia ya isa birnin Bangui jumma’an nan bayan ya baro Casablanca na kasar Maroko, ko da dai a jamhuriyar Benin yake zaman mafaka tun barin mulkinsa.

Jagoran na ‘yan tawaye da ya samu tarbar akalla magoyabansa 30, bayan saukarsa daga jirgin saman kasar Maroko, da rakiyar jami’an ‘yan sanda da sojoji, ana sara ganawarsa da shugaban kasar Faustin – Archange Touadera nan gaba kadan.

Da yake jawabi da ‘yan jaridu, Djotodia yace, shekarar 2020 ta zaman lafiya ce, inda yace daga ‘yanzu ya kawo karshen tawaye tare da kiran mayakan tawaye da su ajiye makamansu.

A shekarar 2013, kazamin rikici ya barke tsakanin mayakan Michel Djotodia wato Seleka dake da magoya bayan musulmai, da kuma Anti Balaka na kiristoci da ake ganin tsohon shugaban kasar Francois Bozize ne ya kafata.

Rikicin da ya haifar da asarar dunbin rayuka, da dukiyoyi, wanda har sai da dakarun Faransa da tayiwa kasar mulkin mallaka ta kawo dauki.

Michel Djotodia ya yi murabus a watan Janairun shekarar 2013, sakamakon matsinlamba daga kasashen duniya, inda aka zabi Touadera a matsayin sabon shugaban kasar a shekarar 2016.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.