Afrika

Majalisar Tunisia ta yi watsi da sunayen Ministoci da aka gabatar

Sabon shugaban kasar Tunisia Kais Saied
Sabon shugaban kasar Tunisia Kais Saied REUTERS/Zoubeir Souissi

Majalisa a Tunisia ta yi watsi da sunayen Ministocin da aka gabatar mata a baya.Bayan share dogon lokaci ana tafka muhawara,yan Majalisun sun kada kuria’a, inda yan majalisu 109 suka kada kuri’ar kin amincewa, yayinda yan majalisu 72 suka yi na’am da wadanan sunaye.

Talla

A hukumace Shugaban kasar Kais Saied cikin kwanaki goma zai sake nada wani sabon Firaminista,wanda zai sake gabatar da sunayen wasu daga Minstocin da za su taimaka masa,idan hakan bata samu Shugaban kasar zai sake kiran wani sabon zabe na yan Majalisu a kasar ta Tunisia.-

Ranar 15 ga watan Nuwamba ne Shugaban kasar ya nada Habib Jemil daga bangaren Ennahdha wanda ya kuma fitar da sunayen Ministocin sa ranar 2 ga wannan watan da muke cikin sa, Sunayen da yan majalisa suka bayyana adawar su a kai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.