Isa ga babban shafi
Najeriya

MDD ta koka kan karuwar jami'an agajin da Boko Haram ke kashewa

Wasu jami'an agaji dake aiki a yankin arewa maso gabashin Najeriya.
Wasu jami'an agaji dake aiki a yankin arewa maso gabashin Najeriya. OCHA/Yasmina Guerda/File Photo/REUTERS
Zubin rubutu: Nura Ado Suleiman
Minti 2

Majalisar dinkin duniya ta yi Allah wadai da hare-haren ta’addancin da ake kaiwa jami’an agaji a yankin arewa maso gabashin Najeriya.

Talla

Shugaban kula da ayyukan jinkai na majalisar ta dinkin duniya a Najeriya, Mista Edward Kallon ne ya bayyana haka, bayanda kididdiga ta nuna cewar, adadin jami’an agajin da masu tayar da kayar baya suka kashe a 2019 ya ninka adadin na 2018.

A shekarar 2018 mayakan Boko Haram sun halaka jami’an agaji 6, yayinda a 2019 suka kashe jami’an 12.

Babban jam’in na majalisar dinkin duniya, ya bayyana rashin samun kyakkyawan tsaro a yankunan da jami’an agajin ke gudanar da ayyukansu, a matsayin abinda ke kan gaba wajen haddasa karuwar rasa rayukansu a yankin arewa maso gabashin na Najeriya.

Wani batu da Mista Edward Kallon ya ja hankali kuma akai, shi ne yadda ake samun yawaitar shingayen binciken da kungiyoyin sa kai masu makamai marasa alaka da gwamnati ke kafawa a kan hanyoyin jihohin Borno da kuma Yobe, matakin da ya ce yana jefa jami’an agajin da sauran fararen hula cikin fuskantar hadarin kashewa ko kuma sace su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.