Sudan

Sudan ta kudu ta gaza kulla yarjejeniyar sulhu da 'yan tawaye

Shugaba Salva Kiir na Sudan ta kudu tare da tawagar gwamnatinsa da bangaren 'yan tawaye.
Shugaba Salva Kiir na Sudan ta kudu tare da tawagar gwamnatinsa da bangaren 'yan tawaye. UN Photo/Eskinder Debebe

Masu shiga tsakanin bangarori masu rikici da juna a Sudan ta Kudu sun ce, gwamnati da ‘yan tawaye da ke tattaunawa sun sake gazawa wajen rattaba hannu kan yarjejeniyar kafa gwamnatin hadin gwiwa, bayan kasa cimma daidaito kan fitar da iyakokin cikin kasar.

Talla

Da dama daga cikin masu sharhin da ke bibiyar lamurran kasar dai sun soki shugaba mai ci Salva Kiir da yiwa taswirar iyakokin jihohin kasar kwaskwarima da nufin ci gaba da mamaye madafun iko, matakin da ya haifar da cikas ga tattaunawar sulhu tsakaninsa da tsohon madugun ‘yan tawaye Riek Machar.

Bayan samun yanci daga Sudan a 2011, an kasafta Sudan ta Kudu zuwa jihohi 10, wadanda aka kara yawansu zuwa 32 a yanzu, sai dai a yanzu tsohon madugun ‘yan tawaye Riek Machar ne neman maida yawan jihohin zuwa 10 ko kuma 21.

Tun a shekarar 2018 shugaba Salva Kirr da Riek Machar suka sa hannu kan yarjejeniyar sulhu, sai dai kawo yanzu sau 2 suna gaza mutunta wa’adin kafa gwamnatin hadin gwiwa, duk da kokarin yin hakan a watan Nuwamban bara, lokacin da aka kara musu tsawon wa’adin da kwanaki 100.

David Mabuza, mataimakin shugaban Afrika ta Kudu, dake jagorantar masu shiga tsakanin a tattaunawar da ke gudana a birnin Juba, ya ce duk da gaza rattaba hannu kan yarjejeniyar, shugaba Kiir da Machar sun amince da shiga wata sabuwar tattaunawar tsawon mako guda domin sasantawa kan raba iko da jihohin kasar da kuma iyakokinsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.