Najeriya-Boko Haram

Tubabbun 'yan Boko Haram 608 na karbar horon komawa cikin jama'a

Wasu tubabbun mayakan Boko Haram.
Wasu tubabbun mayakan Boko Haram. REUTERS/Ahmed Kingimi

Ma’aikatar tsaron Najeriya kasar ta tabbatar da cewa yanzu haka akwai tubabbun mayakan Boko Haram akalla 608 da ke karbar horo na musamman don komawa cikin al’umma karkashin shirin Operation Safe Corridor can a jihar Gombe.

Talla

Birgediya Janar Musa Ibrahim da ke matsayin kwamandan rundunar ta OSC ya ce tsaffin mayakan na boko haram 14 sun fito daga kasashen Kamaru Chadi da Jamhuriyar Nijar, yayinda sauran 596 ke matsayin cikakkun ‘yan Najeriya.

A cewar Birgediya Janar Musa Ibrahim da ke jawabi ga shugaban hukumar raya yankin Arewa mao gabashin Najeriyar, Mr Mohammed Alkali yanzu haka sun yaye mutum 286 daga cikin tsaffin mayakan na boko haram 893 da aka faro shirin da su, wadanda ya ce tuni suka koma cikin al’ummarsu don ci gaba da rayuwa.

Janar Ibrahim ya ba da tabbacin cewa an horar da jami'an ne bisa tsarin rundunar karkashin ka'idojin kasa da kasa wajen ganin basu zama barazana ga al'umma.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.