Isa ga babban shafi
Najeriya-Ghana

Ba yanzu zan bude iyakoki ba - Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari. AFP/SAUL LOEB
Zubin rubutu: Michael Kuduson
Minti 2

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce ba yanzu ne za a sake bude iyakokin kasar da ya garkame ba har sai rahoton kwamitin da aka kafa kan lamarin ya zo hannu.

Talla

A ranar Litinin ya bayyana haka a wata tattaunawa da shugaban Ghana Nana Akufo – Addo a Landan, a gefen taron tattalin arziki na 2020 tsakanin Birtaniya da kasashen Afrika.

Buhari ya ce kwarya – kwarya rufe iyakokin kasar da ya yi, mataki ne na dakile shigowa da makamai da muggan kwayoyi ke yi kasar, amma ba don shinkafa ba.

Shugaban na Najeriya ya ce ba shi yiwuwa ya zuba ido yana kallon matasan kasar sa na tabewa ta wurin ta’ammali da muggan kwayoyi, haka ma ba zai bari tsaron kasar ya tabarbare ta wajen kwararar da kananan makamai ke yi cikinta ba.

Ya ce a duk lokacin da aka kama motocin fasakaurin shinkafa a kan iyakar kasar, ana samun kwayoyi masu gusar da hankali da kuma makamai cikinsu.

Duk da cewa ya bayyana takaicinsa ganin yadda rufe iyakokin ke yin mummunan tasiri kan makwaftan Najeriya, ya ce ba zai bar kasar kara zube matasa na tabewa suna shiga hatsari ba.

Shugaban Ghana Nana Akufo- Addo wanda ya bayyana fahimtarsa kan lamarin, ya yi roko da a hanzarta daukan matakan sake bude iyakokin, yana mai cewa Najeriya mahimmiyar kasuwa ce ga wasu kayyakin da ake samarwa daga Ghana.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.