Najeriya

Cutar da ake kyautata zaton Lassa ce ta hallaka likitoci a Kano

Ana kyautata zaton bazuwar cutar ta Lassa da bera ke yadawa a jihar Kano da ke Arewacin Najeriya
Ana kyautata zaton bazuwar cutar ta Lassa da bera ke yadawa a jihar Kano da ke Arewacin Najeriya barbaric.com

Rahotanni daga jihar Kano a Tarayyar Najeriya, ya tabbatar da mutuwar mutane 3 da ake kyautata zaton sun mutu bayan kamuwa da cutar Lassa wadda bera ke yadawa, ciki har da likitocin asibitin koyarwa na Aminu Kano da ke jihar.

Talla

Majiyoyin labarai a jihar ta Kano sun tabbatar da cewa yanzu haka, asibitin na Aminu Kano ya kaddamar da wani bincike don tabbatar da zargin da ya ke na cewa jami’ansa biyu sun mutu ne sanadiyyar cutar ta Lassa bayan duba wata mata mai juna biyu da ta zo daga jihar Bauchi.

Asibitin na Aminu Kano ya tabbatar da cewa likitocinsa biyu Dr Ummul Kulthum Abba da Dr Habibu Musa da suka mutu a ranakun Juma’a da jiya Litinin bayan fama da makamanciyar cuta da ake kyautata zaton Lassa ce, dukkansu biyu sun duba marar lafiyar kwanaki 20 da suka gabata.

Sanarwar da kungiyar likitocin Najeriya NMA reshen jihar Kano ta fitar a yau, ta bayyana cewa yanzu haka akwai likita na 3 cikin wadanda suka duba marar lafiyar tun a farkon watan nan, da shima ke kwance yana jinyar makamanciyar cutar da ta hallaka ‘yan uwansa biyu.

Sanarwar ta NMA ta ce yanzu haka za a binciki lafiyar iyalan likitocin biyu da suka mutu don tabbatar da ganin basu kamu da cutar da ake kyautata zaton ta Lassa ce ba.

A banagre guda sanarwar ta kuma bayyana cewa akwai wasu da dama da a yanzu haka su ke karbar kulawa baya ga gwaje-gwajen lafiya saboda zargin da ake ko sun kamu da cutar.

NMA reshen Kano cikin sanarwar a yau Talata, ta bayyana cewa tuni ta aike da wasu sakamakon gwajin samfurin cutar ga cibiyar hana yaduwar cuta ta Najeriyar don karkare bincike.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.