Isa ga babban shafi
Najeriya

Sama da 'yan Najeriya miliyan 60 ba su iya rubutu da karatu ba

Le président nigérian Muhammadu Buhari lors d'une ocnférence de presse après sa rencontre avec le président sud-africain Cyril Ramaphosa, à Pretoria, le 3 octobre 2019.
Le président nigérian Muhammadu Buhari lors d'une ocnférence de presse après sa rencontre avec le président sud-africain Cyril Ramaphosa, à Pretoria, le 3 octobre 2019. REUTERS/Siphiwe Sibeko
Zubin rubutu: Michael Kuduson
Minti 2

Hukumar kula da ilimantar da ‘yan kasa a Najeriya ta ce fiye da ’yan Najeriya miliyan 60 ne ba sa iya rubutu da karatu cikin kowane yare.

Talla

Babban sakataren wannan hukumar, Farfesa Abba Abubakar Haladu wanda ya bayyana haka a wani taro a birnin tarayyar kasar Abuja, ya ce kasar na fuskantar kalubalen da ta kai ga dimbim manya da matasa ba sa iya hada harrufa su bada ma’ana.

Ya ce wannan ne ma ummul’aba’san rashin ci gaba a kasar, duba da yawan manya da matasa da wannan al’amari ya shafa.

Ya ce idan har ana bukatar kasar ta bunkasa a fannoni da dama, dole ne dukkan mutanen kasar su iya rubutu da karatu da kuma lissafi a ko ina suke, kuma ko menene jinsin su.

Ministan ilimi na kasar, Malam Adamu Adamu ya ce wajibi ne a dauki matakan gaggawa don kawo sauyi ganin yadda yawan yaran dake barin makaranta ke karuwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.