Isa ga babban shafi
Nijar

Nijar:An dakatar da aikin rijista saboda rashin tsaro

Salah Habi, ministan sadarwar Nijar
Salah Habi, ministan sadarwar Nijar Onep
Zubin rubutu: Abdoulaye Issa
1 min

Hukumar zabe a Jamhuriyar Nijar ta sanar da dakatar da shirin yiwa yan kasar rijistar zabe mai zuwa a yankunan Abala da Tondikiwindi da Makalondi da Torodi da Gouroual da Diagourou da Inates da kuma Banibangou dake Tillaberi sai kuma Tillia dake yankin Tahoua saboda dalilan tsaro.

Talla

Hukumar tace ta dauki matakin ne domin kare lafiyar jama’a kuma idan hali yayi nan gaba, zata gudanar da aiki a yankunan.

Akalla sojoji 174 yan ta’adda suka kashe a Tillaberi a hare hare guda 3 tsakanin watan Disamba zuwa wannan watan na Janairu.

Salah Habi, ministan sadarwar Nijar, ya bayyana cewar daukar matakin ba zai hana zabe mai zuwa ba.

Hukumar Zabe a Nijar ta sanar da dakatar da shirin yiwa yan kasar rijistar zabe mai zuwa

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.