Najeriya-Lassa

Cutar Lassa ta fantsama zuwa jihohin Najeriya 9

Yanzu haka akwai adadin jumullar mutane 121 da ke dauke da cutar a sassan Najeriya.
Yanzu haka akwai adadin jumullar mutane 121 da ke dauke da cutar a sassan Najeriya. wikimedia

Rahotanni daga Najeriya sun tabbatar da yadda annobar cutar Lassa da bera ke yadawa ta bazu zuwa jihohin kasar 9 yayinda yanzu ake da adadin mutane 121 da ke dauke da ita bayan wasu da cutar ta kashe.

Talla

Majiyar labarai a Najeriyar ta tabbatar da jihar Ondo a matsayin kan gaba wajen yawan masu dauke da cutar da adadin mutum 89 kana Edo mutane 18 sai Ebonyi mutum 5 tukuna Taraba 5 dukkanninsu dauke da cutar.

Sauran jihohin da aka tabbatar da masu dauke da cutar ta Lassa sun hadar da Kano da adadin mutum 3 sai Plateau da ke da adadin mutane 2 masu dauke da cutar tukuna jihohin Bauchi da Ogun da Delta kowanne mutum 1.

A cewar majiyar labaran a Najeriya, akwai tarin mutane a jihohin Kano da Ondo wadanda ke karbar kulawa da gwaje-gwaje na musamman don tabbatar da ko suna dauke da cutar bayan mu'amalarsu da masu dauke da cutar ta Lassa.

Cutar ta Lassa wadda ko a bara ta kashe tarin jama'a a kudancin Najeriyar, mahukunta sun tabbatar da daukar matakan gaggawa don yakarta baya ga daukar matakan wayar da kan jama'a game da hanyoyin da za su bi wajen kare kansu.

Masana lafiya dai sun bayyana alamomin cutar da zazzabi, ciwon kai, kasala, tari, kaikayin makogwaro ko kuma mura baya ga amai da gudawa.

Masanan dai sun bukaci al'umma su kauracewa barin wurare da kazanta baya ga wanke hannu a duk lokacin da za su kai wani abu bakinsu.

A bangare guda masanan sun kuma yi gargadi kan shanya abinci da al'umma ke yi musamman a yankunan karkara don gudun kada bera ya bi ta ka da nufin kariya daga cutar, yayinda suka kuma ja hankalin jama'a kan kan barin abinci a bude.

 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.