Taron sulhunta rikicin Libya a Algeria
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
A birnin Algiers na Algeria, yau alhamis ministocin harkokin wajen kasashe 5 masu makoftaka da Libya, na gudanar da taro don tattauna rikicin kasar ta Libya.
Kasashen da ke halartar taron sun hada da Tunisia, Masar, Chadi, Nijar da kuma Sudan, sai kuma takwaransu na Jamus Heiko Maas wanda ya yi masu karin bayani a game da muhimman batutuwan da aka cimma matsaya a taron da aka yi ranar lahadi a birnin Berlin.
Abdoulakarim Ibrahim Shikal ya tambayi Dr Nouhou Salihou Jangorzo, sanin ko akwai rawar da wadannan kasashe za su iya takawa don samar da zaman lafiya a Libya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu