Myanmar-Rohingya

Hukucin ICJ kan Myanmar nasara ce ga duniya - Gambia

Wasu daga cikin 'yan kabilar Rohingya dake gudun hijira a Bangladesh.
Wasu daga cikin 'yan kabilar Rohingya dake gudun hijira a Bangladesh. REUTERS/Hannah McKay

Gwamnatin Gambia ta hannun ministan shari’arta Abubacarr Tambadou, ta yabawa kotun duniya ICJ bisa hukuncin da ta yanke, na baiwa gwamnatin Myanmar umarnin tilas ta dauki matakan kare kabilar Rohingya Musulmi dake kasar daga kisan kare dangi, da sauran laifukan yaki.

Talla

Yayin jawabi ga manema labarai, Minstan Shari’ar na Gambia, ya bayyana hukuncin a matsayin muhimmin tarihi ga ‘yan kabilar Rohingya da ma duniya baki daya.

Wannan dai shi ne karo na farko da kotun duniyar ta soma daukar matakin kawo karshen halin da ‘yan Kabilar ta Rohingya suka tsinci kansu tun daga 2017.

Yayin yanke hukuncin, jagoran alkalai 17 dake kotun, mai shari’a AbdulQawi Ahmed Yusuf ya ce hujjoji sun nuna cewar har yanzu ragowar ‘yan kabilar ta Rohingya dake Maynmar na cikin mummunan hadari, dan haka ya zama dole a basu kariya daga ci gaba da yi musu kisan kiyashi.

A karshen shekarar bara kasar Gambia mai rinjayen Musulmi ta shigar da kara gaban kotun duniyar, inda ta nemi a hukunta gwamnatin Myanmar biyo bayan matakin sojojin kasar na cin zarafi da yiwa ‘yan Kabilar Rohingya kisan kare dangi, abinda ya tilastawa sama da dubu 750 tserewa zuwa Bangladesh, wadanda kuma suka tabbatar da rahotannin yadda, sojojin na Myanmar da mayakan sa kai mabiya addinin Buddha, suka rika cin zarafinsu ta hanyar fyade da kuma azabtarwa.

Yanzu haka dai kotun duniyar ta baiwa gwamnatin Myanmar umarnin cewa tilas ta dauki matakan hana dakarunta da saauran kungiyoyin sa kai, aikata dukkanin abubuwan da majalisar dinkin duniya ta alakanta shi da kisan kare dangi, ko laifin yaki, yayin babban taronta na shekarar 1948.

Sama da kasashe 50 ciki har da Canada da Netherlands ne ke marawa Gambia baya kan karar gwamnatin Myanmar da ta shigar gaban kotun duniyar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.