Afrika

Samar da kudi bai daya alheri ne ga kasashen mu

Elhaj Mutari Ali Daura, Jami'in Diflomasiya
Elhaj Mutari Ali Daura, Jami'in Diflomasiya RFI/Hausa/Dr Meddy

Wasu Kasashen yammacin Afrika masu amfani da kudin CFA sun shigar da bukatar gani sun daina yi amfani da wannan kudin tun shekarar da ta shude, al’amarin ya sanya kasashen yankin nazari don cimma jituwa tsakanin su,yayinda wasu kasashen renon ingila suka bayyana bacin ran su.

Talla

A hukumance a wannan shekara ta 2020 ne kasashen da suka amince da sabuwar takarda ta kudin Eco zasu soma mfani da wannan sabuwar takarda a karkashin inuwar babban bankin Faransa.
Daga cikin kasashen da suka bayyana rashin amincewar sun a ci gaba da kasancewa a karkashin inuwar bankin Faransa, Gabon ta bakin Ministan kudin kasar ya bukaci kasashen dake amfani da kudin CFA sunyi watsi da wannan bukata.

Kudin cfa na ci gaba da jan hankulan gwamnatocin kasashe, Regis Immongault ministan kudin Gabon a wata zantawa da manema labarai ya bayyana cewa ficewar kasashe ko kuma neman canza kudin cfa da wanin kudin can daban ba karamar ila bace ga kasashen.
A cewar ministan, kudin cfa ya taimaka wajen karfafa damkon zumunci dama habaka tattalin arzikin kungiyar kasashe masu amfani da kudin.

An dai bayyana cewa kusan mutane milliyan 155 daga kasashen yamacin Afrika 15 ne ke amfani da kudin cfa.

A shekara ta 1945 aka kaddamar da kudin na cfa,inda turawan mulkin malaka suka bukaci kasashen Afrika musaman na yammaci sun ajiye dukkanin kudaden ajiyar su a asunsun kasar Faransa,wanda a lokacin wasu daga yankin Afrika dama Duniya suka nuna adawa a kai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI