Isa ga babban shafi
Mali

'Yan ta'adda sun kashe jami'an tsaron Mali da dama

Wasu dakarun sojin kasar Mali a garin Gao.
Wasu dakarun sojin kasar Mali a garin Gao. AFP/Souleymane Ag Anara
Zubin rubutu: Nura Ado Suleiman
1 min

Rundunar sojin Mali ta ce, Jandarmomin kasar 19 sun rasa rayukansu, wasu 5 kuma sun jikkata yayin farmakin da ‘yan ta’adda suka kaiwa sansaninsu da ake kira da Sokolo a yankin tsakiyar kasar.

Talla

Wani ganau ya ce maharan da adadinsu ya zarta 100, sun afkawa sansanin Jandarmomin ne akan babura, inda suka yiwa musu kawanya.

Sansanin Jandarmomin na Sokolo na yankin Segou, inda yayi kaurin suna wajen fama da hare-haren kungiyoyin mayaka masu biyayya ga, Al-Qaeda.

Farmakin na baya bayan nan a Mali ya zo ne dai dai lokacin da ministar tsaron Faransa Florence Parly ke ziyara a birnin Washington domin tattaunawa da gwamnatin Amurka, don neman soke matakin kwashe sojojin kasar daga Sahel, wato yammacin Nahiyar Afrika, inda dakarun Faransa suka shafe shekaru suna kokarin murkushe ta’addanci.

Kafin ziyarar a Washington, ministar tsaron Faransar tayi tattaki zuwa yankin na Sahel dake fama da hare-haren ‘yan ta’adda, wadanda a baya bayan nan suka halaka dakarun jamhuriyar Nijar sama da 150.

A shekarar 2012 Faransa ta soma girke dakarunta dubu 4 da 500 a Mali, domin murkushe masu tada kayar bayan da suka so hambarar da gwamnati, wadanda kuma a yanzu ke iko da yanki mai fadi daga arewacin kasar.

Yanzu haka kuma aikin samar da tsaron dakarun na Faransa ya fadada zuwa Burkina Faso, Niger, Chadi da kuma Mauritania.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.