Isa ga babban shafi

Kuskure ne Najeriya ta rika kwarmata salon farmakar 'yan ta'adda-Dambazau

Jirgin yakin Sojin Saman Najeriya da za a fara aikin farmakar 'yan bindiga da su.
Jirgin yakin Sojin Saman Najeriya da za a fara aikin farmakar 'yan bindiga da su. naij.com
Zubin rubutu: Azima Bashir Aminu
1 min

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bada umurnin amfani da jiragen yaki domin kai hari kan Yan bindigar dake garkuwa da mutane da kuma kashe makiyaya suna sace musu shanu a Jihar Niger.

Talla

Buhari wanda ya bayyana hare haren a matsayin abin takaici, ya ce jiragen za su dinga aiki ne a iyakokin Jihohin Kaduna, Niger da Zamfara da ke fama da wannan matsala.

Dangane da wannan mataki, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Janar Idris Bello Dambazau mai ritaya, wanda kuma ya bayyana matakin kwarmata dabarun kai farmakin a matsayin ankarar da 'yan ta'addan su sauya maboya.

Kuskure ne Najeriya ta rika kwarmata salon farmakar 'yan ta'adda-Dambazau

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.