Masar

Kotun Masar ta yanke hukuncin kisa kan tsohon sojanta

Jami'an tsaron Masar yayin tafiya da tsohon sojan kasar Hisham Ashmawy, wanda ya rikide zuwa dan ta'adda.
Jami'an tsaron Masar yayin tafiya da tsohon sojan kasar Hisham Ashmawy, wanda ya rikide zuwa dan ta'adda. AFP

Kotu a Masar ta yanke hukuncin kisa kan wani tsohon jagoran sojin kasar Hisham al-Asmawy, tare da wasu mutane 36, bayan samunsu da laifukan ta’addanci.

Talla

A karshen shekarar 2018 sojin Libya masu biyayya ga Janar Khalifa haftar suka kame Ashmawy a gabashin kasar, tare da mika shi da Masar cikin watan Mayun shekarar bara.

Daga cikin tuhume-tuhumen da Ashmawy ya fuskanta, akwai shirya harin ta’addancin da ya halaka sojojin Masar 22 akan iyakarsu da Libya cikin shekarar 2014, sai kuma yunkurin kashe tsohon ministan cikin gidan Masar a shekarar 2013.

A shekarar ta 2014 ne kuma kungiyar Ansar Bayt-Maqdis da Hisham Ashmawy ya jagoranta ta yi mubaya’a ga kungiyar IS.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.