Tanzania

Turmutsitsi: Mutane 20 sun mutu a wani cocin Tanzania

Misalin turmutsitsi
Misalin turmutsitsi Reuters/路透社

Akalla mutane 20 ne aka tattake har lahira a wani turmutsitsi da ya auku a wani coci a arewacin Tanzania kamar yadda hukumomi suka bayyana a Lahadin nan.

Talla

Kamfanin dillancin labaran Faransa ta ruwaito wani jami’in gwamnati Kippi Warioba, wanda kwamishina ne a yankin yana bayyana fargabar adadin wadanda suka mutu a lamarin da ya auku a jiya Asabar na iya karuwa.

Wannan mummunan al’amari ya auku ne lokacin da da dimbim masu bauta suke halartar wani taron addu’o’i a ranar Asabar, wanda wani fitaccen mai wa’azin addinin Kirista, Boniface Mwamposa, shugaban cocin Arise and Shine Ministry na Tanzania ke jagoranta.

Turmutsitsin ya faru ne yayin da Mwamposa, wanda ake wa inkiya da "Apostle", ya zuba wani mai, wanda ya ce yana cike da tsarki a kasa, su kuma mutanen da ke halartar taron suka yi ta rige rigen tabawa don samun waraka daga cututtuka kamar yadda suke kyautata zato.

Wata ganau, Jennifer Temu, ta shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa cewa daga nan ne fa aka shiga turereniya inda wasu suka fadi, aka kuma tattake su suka mutu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.