Isa ga babban shafi
Faransa

Faransa za ta tura karin dakaru 600 zuwa yankin Sahel

Wasu sojojin Faransa yayin sintiri a dajin Tofa Gala dake arewacin kasar Burkina Faso a yankin Sahel.
Wasu sojojin Faransa yayin sintiri a dajin Tofa Gala dake arewacin kasar Burkina Faso a yankin Sahel. MICHELE CATTANI / AFP
Zubin rubutu: Nura Ado Suleiman
1 min

Faransa ta bayyana shirin tura karin sojinta sama da 500 zuwa yankin Sahel, inda a yanzu haka dakarunta dubu 4 da 500 ke yakar kungiyoyin ‘yan ta’adda.

Talla

Ministar tsaron Faransa Florence Parly ce ta bayyana shirin, tare da karin bayanin cewar, za a tura karin dakarun 600 zuwa yankin na Sahel ne nan da karshen watan Fabarairu da muka shiga.

Parley tace za a girke karin sojojin na Faransa a yankin da ya hada iyakokin Mali, Burkina Faso da kuma Nijar, domin murkushe barazanar hare-haren ta’addancin dake karuwa a yankin.

A wata sanarwar kuma rundunar sojin kasar ta Faransa tace za ta aika da karin dakarunta zuwa Sahel ne tare da motocin sulke kimanin 100.

A baya bayan nan dai kasashen Nijar, da Burkina Faso suka fi fuskantar hare-haren ta’addanci, inda a jamhuriyar ta Nijar kadai ‘yan ta’addan suka halaka sojoji sama da 150 a kasa da watanni 2, a hare-haren da suka kaiwa sansanonin sojin kasar a Inates da kuma Shinagodar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.