Najeriya

'Yan bindiga sun kakkabo jirgin 'yan sanda bayan kashe 'yan bindiga 250

Wasu 'yan bindiga a Najeriya.
Wasu 'yan bindiga a Najeriya. REUTERS/Goran Tomasevic/File Photo

Rundunar 'yan sandan Najeriya ta sanar da cewar wasu 'yan bindiga a yankin Birnin Gwari da ke Jihar Kaduna sun harbo mata jirgin sama mai saukar ungulu bayan da ya kai musu hari inda ya hallaka sama da 'yan bindiga 250 daga cikin su.

Talla

Mai Magana da yawun rundunar Frank Mba ya ce jirgin wanda ke cikin masu kai hare hare kan 'yan bindigar da suka addabi Jihar ya gamu da hari daga 'yan bindigar da ke amfani da na’uarar kakkabo jirage da kuma manyan bindigo abinda ya sa matuka jirgin suka yi amfani da kwarewar su wajen sauka a tashar sojin sama da ke Kaduna.

A cewar mai magana da yawun rundunar 'yansandan ta Kaduna yanzu haka an kwashe matukan jirgin domin kula da lafiyar su sakamakon raunin da suka samu, yayin da aka dauki jirgin zuwa Abuja.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.