Nijar-Agadez

Agadez ta yi bikin tunawa da wadanda suka mutu a kokarin shiga Turai

Akalla 'yan cirani dubu 6 suka mutu a tekun Mediterranean cikin shekaru 5 a kokarinsu na tsallakawa Turai.
Akalla 'yan cirani dubu 6 suka mutu a tekun Mediterranean cikin shekaru 5 a kokarinsu na tsallakawa Turai. Studio graphique FMM

Hukumar de ke kula da bakin haure ta Majalisar Dinkin duniya OIM, ta ce kusan mutane dubu 6 suka mutu a tekun Meditareniya a kokarin su na ketarawa Turai cikin shekaru 5, duk da cewa an samu ragowar adadin mutanen da ke rasa rayukan su a ‘yan tsakanin nan.Garin Agadez ya kasance wata hanya da bakin ke anfani da ita don cimma burin su, kuma domin tunawa da wadanda suka rasa rayukansu ta wannan hanya, kungiyoyi sun gudanar da bikin tunawa da wadanda suka rasa rayukansu ta wannan hanya tare da wayar da kan jama'a kan hadarin ketarawa da nufin shiga Turai. daga Agadez ga rahoton Umar Sani.

Talla

Agadez ta yi bikin tunawa da wadanda suka mutu a kokarin shiga Turai

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.