Afrika

Guterres ya bayyana goyan baya don sassanta rikicin Libya daga AU

Antonio Guterres,a lokacin da yake tattaunawa da France 24  da RFI
Antonio Guterres,a lokacin da yake tattaunawa da France 24 da RFI RFI-France 24

A wata tattaunawa da ya yi da RFI da France24, Babban sakataren Majalisar dinkin duniya Antonio Guterres,ya yi kashedin kara gurbacewar matsalar tsaro a yankin Sahel, idan Amruka ta jaye sojojinta daga yankin.

Talla

Antonio Guterres ya bukaci kafa rundunar tsaro da zata samu goyon bayan kasashen Duniya, domin yakin da yan ta’addan dake neman durkusar da babban yankin na Sahel yanzu haka.

Rikicin Libya na daya daga cikin matsalolin dake tayar da hankulan Antonio Guterres,wanda ya kuma bayyana cewa ya zama dole a baiwa kungiuyar kasashen Afrika damar taka gaggarumar rawa don kawo karshen wannan rikici da wasu can daban a Afrika.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.