Afrika

Kotun Faransa taci tarar Teodorin Obiang

Teodorin Obiang, dan Shugaban kasar Equatorial Guinee
Teodorin Obiang, dan Shugaban kasar Equatorial Guinee Michele Spatari / AFP

Wata kotun daukaka kara a Faransa taci tarar dan shugaban kasar Equatorial Guinea Teodorin Obiang euro miliyan 30 da kuma masa daurin talala saboda samun sa da laifin almubazzaranci da dukiyar talakawan kasar, bayan ta kwace kadarorin da ya mallaka.

Talla

Tun a shekarar 2017 kotu ta samu Obiang da laifin rayuwar kasaita da dukiyar jama’a wajen sayen motocin kawa da gidajen kasaita.

Rashin gamsuwa da hukuncin karamar kotun ya sa Obiang ya daukaka kara, amma kotu tayi watsi da karar inda ta tabbatar da hukuncin.

Masu gabatar da kara sun ce dan shugaban ya halarta kudaden haramun da suka kai euro miliyan 150 a Faransa, bayan wani bene mai hawa 6 da ya mallaka tare da wani katafaren gida.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.