Kamaru-Human Right Watch

'Yan awaren Kamaru sun sace fiye da mutum 100 gabanin zabe- HRW

Wani bangare na yankin kudu maso yammacin kasar Kamaru yayin zaben 'yan majalisun da ya gudana.
Wani bangare na yankin kudu maso yammacin kasar Kamaru yayin zaben 'yan majalisun da ya gudana. Crisis Group

Kungiyar kare hakkin Dan adam ta Human Rights watch ta ce mayakan 'yan awaren Kamaru sun sace mutane sama da 100 da kuma kona tarin kadarori kafin zaben 'yan majalisun da akayi a karshen mako.

Talla

Daraktan kungiyar da ke kula da tsakiyar Afirka, Lewis Mudge ya ce ya zama wajibi shugabannin 'yan awaren su bayyanawa magoya bayan su karara cewar su daina kai hare hare kan fararen hula.

Mudge ya kuma ce suma dakarun gwamnati sun cigaba da azabtar da mutane a Yankunan da ake amfani da Turancin Ingilishi, inda ya bukaci gwamnatin da ta ja kunnen dakarun ta da su daina cin zarafin Bil Adama.

Kungiyar ta bukaci hukunta wadanda ake zargi da aikata laifuffuka daga cikin jami’an tsaron.

Rikici ya barke ne a bangaren 'yan awaren shekaru biyu da suka gabata, inda su ke korafi kan yadda ake nuna musu banbanci, matakin da ya haifar da arangama da jami’an tsaro wanda ya kai ga mutuwar mutane akalla 3,000, kana ya raba mutane sama da 700,000 da gidajen su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.