Najeriya-Amnesty

Amnesty ta nemi bin diddigin zargin Sojin Najeriya da kone kauyuka 3

Wasu Sojin Najeriya a Maiduguri.
Wasu Sojin Najeriya a Maiduguri. STEFAN HEUNIS/AFP

Kungiyar kare hakkin bil’adama ta Amnesty International, ta bukaci a gudanar da bincike game da bayanai da ke cewa sojojin Najeriya sun kona kauyuka uku kurmus a jihar Borno tsakanin ranar 3 zuwa 4 ga watan janairun da ya gabata.

Talla

Amnesty International ta ce ta samu wadannan bayani ne daga mutane 12 da suka hada da maza da mata, wadanda suka shaidi yadda lamarin ya faru, sannan kuma akwai wasu hotunan da tauraron dan adam ya dauka da ke tabbatar hakan.

Kungiyar ta ce da farko sojojin sun kori daruruwan mutanen da ke rayuwa a wadannan kauyuka da ke kan hanyar Maiduguri zuwa Damaturu, kafin daga bisani su cinna wa gidaje wuta don kona su kurmus.

Amnesty ta ci gaba da cewa illahirin mazauna wadannan kauyuka ne sojoji suka kwashe a cikin manyan motoci inda suka jigbe su a wani sansanin ‘yan gudun hijira da ke garin Maiduguri.

Daraktan Amnesty International a Najeriya Osai Ojigho, ya ce da wadannan bayanai, akwai bukatar gudanar da bincike dangane da yiyuwar aikata laifufukan yaki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.