Kamaru

Dubban 'yan Kamaru sun tsere zuwa Najeriya

Wasu 'yan gudun hijirar Kamaru a Najeriya.
Wasu 'yan gudun hijirar Kamaru a Najeriya. AFP PHOTO / REINNIER KAZE

Hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce akalla mutane dubu 8 ne suka tsere daga Kamaru zuwa Najeriya cikin makonni biyu da suka gabata.

Talla

Hukumar tace kwararar dubban ‘yan gudun hijirar ya biyo bayan tsanantar fada tsakanin sojin gwamnatin da ‘yan awaren kasar ta Kamaru.

Rahoton yayi karin bayanin cewar ‘yan gudun hijirar na baya bayan nan da suka tsere zuwa Najeriya sun samu mafaka ne a jihohin Taraba da Cross Rivers, abinda ya sa adadin ‘yan kasar ta Kamaru da suka tserewa rikicin ‘yan awaren zuwa Najeriya kaiwa dubu 60.

A cikin watan oktoban shekarar 2017, rikicin makamai ya barke a yankin ‘yan aware masu magana da turancin ingilishi a arewaci da kudancin kasar ta Kamaru dake kan iyaka da Najeriya, yankin da mayakan ke neman ballewa daga masu magana da harshen Faransancidon kafa kasarsu.

Hukumar ta kiyasta cewa sama da mutane dubu 679 suka rasa matsuguninsu sakamakon rikicin ‘yan awaren, yayinda kididdigar kungiyoyi masu zaman kansu ta nuna sama da rayuka 3000 ne suka salwanta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.