Isa ga babban shafi
Najeriya

Zanga-zanga ta tilasta 'yan sanda sanya dokar hana fita a Bayelsa

Wasu jami'an 'yansandan Najeriya.
Wasu jami'an 'yansandan Najeriya. Gulf Times
Zubin rubutu: Azima Bashir Aminu
1 min

'Yan sanda a Najeriya sun kafa dokar hana fita a Jihar Bayelsa sakamakon wata kazamar zanga zangar da ta barke a birnin Yenagoa sakamakon sanar da Sanata Duoye Diri a matsayin zababben Gwamnan Jihar da hukumar zabe ta yi.

Talla

Rahotanni sun ce matasa sun yi ta kone kone da lalata gine ginen gwamnati abinda ya tilasta kwamishinan 'yan Sanda Uche Anozie tare da jami’an sa sintiri akan tituna domin tabbatar da zaman lafiya.

Kwamishinan ya ce sun kama mutane 8 daga cikin masu zanga zangar, yayin da aka kafa dokar hana fita a kananan hukumomi 8 da ke Jihar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.