ECOWAS-CEDEAO

Ministocin ECOWAS sun gana kan rufe iyakokin Najeriya

Hedikwatar kungiyar kasashen Yammacin Afrika ECOWAS.
Hedikwatar kungiyar kasashen Yammacin Afrika ECOWAS. TheNiche

Ministocin kasashen yammacin Afrika suka yi taro kan lalubo hanyar kawo karshen matsalolin da ya sanya Najeriya daukar matakin rufe kan iyakokinta na kan tudu.

Talla

Sai dai bayan kammala taron, ministocin basu yi karin bayani kan matakai ko shawarwarin da suka yanke kan batun rufe iyakokin Najeriyar ba.

Cikin watan Agustan shekarar 2019, Najeriya ta rufe kan iyakokinta na kan tudu, matakin da tace ta dauka domin kawo karshen matsalar fasakaurin kayayyakin da take iya samarwa acikin gida.

Tun bayan daukar matakin ne kasashen yammacin Afrika ke kokarin kawo karshen matsalar, la’akari da yadda matakin ke shafar tattalin arzikin kasashen yankin na Yammacin nahiyar ta Afrika, musamman ma masu makwabtaka kai tsaye da Najeriyar, da suka hada da Nijar da kuma Jamhuriyar Benin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.