Sudan ta Kudu

Salva Kiir ya rage adadin jihohin Sudan ta Kudu daga 32 zuwa 10

Shugaban Sudan ta Kudu Salva Kiir yayin gaisawa da tsohon madugun 'yan tawaye Riek Machar.
Shugaban Sudan ta Kudu Salva Kiir yayin gaisawa da tsohon madugun 'yan tawaye Riek Machar. REUTERS/Jok Solomun

Shugaban Sudan ta Kudu Salva Kiir ya amince da bukatar bangaren ‘yan tawaye na rage yawan jihohin kasar daga 32 zuwa 10, daya daga cikin batutuwan da a baya suka haifar da cikas ga shirin kafa gwamnatin hadin gwiwa.

Talla

Yayin sanar da matakin shugaba Kiir ya ce bukata ce mai tsaurin gaske, amma dole a aiwatar da ita, muddin ana bukatar cimma zaman lafiya.

Rashin cimma matsaya guda kan adadin jihohin Sudan ta Kudu da kuma matakan hade rundunoni masu yakar juna ne dai suka kasance, manyan batutuwan da suka haifar da tsaiko ga shirin soma aiwatar da yarjejeniyar sulhu ta din din din tsakanin shugaba Salva Kiir da tsohon madugun ‘yan tawaye Riek Machar.

Tun a watan Nuwanban 2018, bangarorin 2 suka cimma yarjejeniyar sulhun, amma aiwatarwa ya gagara.

A shekarar 2013 yakin basasa ya barke a Sudan ta Kudu bayan ballewarta daga Sudan, bayanda Shugaba Salva Kiir ya zargi mataimakinsa a waccan lokacin wato Riek Machar da yunkurin yi masa juyin mulki, rikicin da ya rikide zuwa na kabilanci daga bisani.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.