Mali

Mahara sun halaka mutane 40 a tsakiyar Mali

Dakarun tsaron Mali na sintiri a yankin Gao na kasar
Dakarun tsaron Mali na sintiri a yankin Gao na kasar AFP/Souleymane Ag Anara

Mahukuntan kasar Mali sun tabbatar da mutuwar mutane 40, ciki harda sojojin kasar 9,sakamakon wasu hare-hare ta'addanci da na kabilanci a yankin tsakiyar kasar

Talla

Dagacin yankin Aly Ousmane Barry ya shaidawa kamfanin Dillancin Labaran kasar Faransa AFP cewar, kimanin ‘yan bindiga 30 suka kai harin kauyen Ogossagou na Fulani Makiyaya, inda aka kashe akalla mutane 30.

Kazalika Majiyar sojin kasar ma ta tabbatar da mutuwar sojoji 9 da jikkatar wasu 4 a yankin Gao, a wani harin mayaka masu ikirarin jihadi.

Da farko an bayyana cewa mutane 11 ne suka rasa rayukansu a harin, to sai dai wani jami’in gwamnatin a yankin ya ce an kirga gawarwakin mutane 20, yayin da wasu akalla 28 suka bata baya ga wadanda aka raunuta.

Ga alama maharan sun yanke shawarar afkawa mazauna garin na Oga-sagou ne sa’o’i kadan bayan da suka samu labarin cewa jami’an tsaron da ke bai wa jama’a kariya sun fice daga garin. Mali dai kas ace da ke fama da ayyukan ta’addanci da kuma rikici tsakanin kabilu.

A watan Maris din shekarar 2019, gungun maharan da ake kyautata zaton ‘yan kabilar Dogon nem suka yiwa Fulani 150 kisan gilla a kauyen na Ogassagou, abinda ya rura wutar rikicin kabilancin da ya addabi kasar Mali, bayaga hare-haren kungiyoyin ‘yan ta’adda.

Al’ummar Mali dake zaune a yankin tsakiyar kasar, na zargin sojoji da gazawa wajen basu kariya daga matsalolin tsaron dake ta’azzara, abinda yayi sanadin tilastawa akalla mutane dubu 200 tserewa muhallansu, yayinda kauyuka da dama a yanzu ke wanzuwa ba tare da samun kulawar jami’an tsaro ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.