Sudan ta Kudu

'Yan tawaye sun yi fatali da tayin sulhu da Gwamnati

Wani sojan Sudan ta Kudu, yayin horas da sabbin jami'an da aka dauka don kafa rundunar hadin gwiwar sojin gwamnati da 'yan tawaye.
Wani sojan Sudan ta Kudu, yayin horas da sabbin jami'an da aka dauka don kafa rundunar hadin gwiwar sojin gwamnati da 'yan tawaye. AFP

‘Yan tawayen Sudan ta Kudu karkashin jagorancin tsohon mataimakin shugaban kasar Riek Machar, sun yi fatali da tayin gwamnati na rage adadin jihohin kasar daga 32 zuwa 10, daya daga cikin batutuwan da suka haifar da cikas wajen kafa gwamnatin hadaka.

Talla

Matakin ‘yan tawayen dai, ya sanya murnar sa ran cimma sulhu na din din din a Sudan ta Kudu komawa ciki, kan fatan kawo karshen yakin basasar kasar da ya salwantar da rayuka akalla dubu 3 da 80.

Tsohon madugun ‘yan tawaye Riek Machar ya bayyana matakin shugaba Kiir na baiwa jihohin Pibo, Ruweng da kuma Abyei, a matsayin dalilin yin fatali da tayin sulhun.

Yanzu haka dai shugaba Kiir da Machar na fuskantar matsin lamba daga kasashen duniya, don kafa gwamnatin hadin gwiwa kafin ranar 22 ga watan Fabarairu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.